CUTAR SHAWARA: Za a fara yin allurar rigakafi a kasar nan

0

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta sanar cewa cutar shawara ta yi ajalin mutane 9 a kananan hukumomi 12 a jihohin Kwara, Kano, Niger, Nasarawa, Kebbi, Kogi da Zamfara.

Bisa ga rahotan da hukumar ta bada, ta bayyana cewa cutar ta fara bullowa ne a watan Satumba 2017 a jikin wata ‘yar shekara 7 daga karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.

Binciken da suka gudanar kuma ya nuna cewa tun da aka haifi wannan yarinya ba a taba yi mata alluran rigakafin cutar shawara ba.

Bayan haka cutar sai ta yadu zuwa jihohi 16 a kasar nan wanda ya hada da Abia, Borno, Kogi, Kwara, Kebbi, Plateau, Zamfara, Enugu, Oyo, Anambra, Edo, Lagos, Kano, Nasarawa, Katsina da Niger.

Sakamakon haka hukumar NCDC ta bayyana cewa ranar 2 ga watan Janairu hukumar ta gwada jinin mutane 230 cikin mutane 358 da ake zaton suna dauke da cutar inda aka gano cewa 63 daga cikin su na dauke da cutar.

Ministan lafiya Isaac Adewole yace gwamanti za ta fara yin allura rigakafin cutar a duk fadin kasar nan.

Daga karshe Adewloe ya yi kira da mutane da su sami karban wannan alluran sannan su tabbatar sun karbi kati mai launi ruwan kwai wato ‘Yello Card’ da turanci wanda ke nuna mutum ya karbi wannan alluran.

Share.

game da Author