Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabin shugabanin manyan asibitoci 4 dake kasan nan.
Ma’aikatan kiwon lafiya ce ta sanar da haka ranar Laraba inda ta lissafo sunayen wadanda aka nada kamar haka;
1 – Ajayi Adekunle a matsayin shugaban asibitin gwamnati dake Ido jihar Ekiti.
2 – Henry Ugboma zai shugabanci asibitin koyarwa na jami’ar Port-Harcourt, jihar Rivers.
3- T.O Adebowale zai shugabanci asibitin mahaukata dake Aro jihar Ogun.
4 – Achigbu Kinsley zai shugabanci babbar asibitin dake Owerri jihar Imo.
Sannan kuma wadanda aka nada din za suyi yi aiki ne har na tsawon shekaru 4.