Buhari ya maida wa Obasanjo Martani

0

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa kila wasu daga cikin dalilan da ya sa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin Buhari shine don bashi da lokaci yin bincike da duba irin nasarorin da gwamnati ta sa mu zuwa yanzu.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata doguwar takarda da ofishin sa ta fitar domin kara wayar wa Obasanjo kai kan nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu zuwa yanzu.

Lai Mohammed ya ce abinda Obasanjo ya fadi, sun karanta kuma ” muna gode masa da samun lokaci da yayi wajen rubuta wannan doguwar wasika.”

Lai Muhammed ya ce an samu nasarori masu yawa a harkar tsaro, samar da ababen more rayuwa, gina kasa da sauran su.

Share.

game da Author