Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Budaddiyar Jami’ar Nijeriya, NOUN ita ce mafita kawai ga dalibai masu son shiga jami’a, ganin cewa sauran jami’o’in kasar nan ba su iya daukar kashi 1 bisa 3 na masu son shiga jami’a a kowace shekara.
Buhari ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar a lokacin da ya ke jawabi wurin bukin yaye dalibai 14,771 da NOUN ta gudanar a harabar hedikwatar jami’ar a Abuja.
Buhari ya ce jami’ar NOUN na kokarin ta wajen tafiyar da tsarin karatu na tafiya yadda ake so a kasar nan.
Daga nan sai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta rika bari ana nuna bambanci tsakanin daliban NOUN da na sauran jami’o’i ba, daga yanzu duk daidai ake.
Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rasheed ne ya wakilci shugaba Buhari.
Da ya juya kan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Buhari ya jinjina masa, ganin yadda ya koma makaranta har ya samu digirin-digirgir. Sai ya kara da cewa, daga yanzu Obasanjo shi ne uban NOUN.
Da ya ke nasa jawabi bayan an damka masa satifikek na shaidar kammala Ph.D. inda ya zama Dakta kenan, Obasanjo ya bayar da labarin irin gaganiyar da sha kafin ya kammala karatun sa.
“Tun da farko da shiga NOUN, na bayyana musu cewa ni koyo na zo ba na zo ba ne a ba ni wani girma ko a rika tula min kasa ba. Na ce kada su bambanta ni ko su ba ni wani fifiko fiye da na sauran dalibai.
“Na rika daukar littattafai na kamar yadda sauran dalibai ke dauka. Na rika rataya jaka ta ko na rike ta kamar yadda sauran dalibai ke daukar ta su. Duk wani ko wata gaganiya da gogayyar da daliban digirin-digirgir ke yi, babu wadda ba a yi da ni ba.
“Na je Yankin Arewa-maso-Gabas na yi binciken kammala karatu, kuma ba sau daya na je ba. Na nemi wadanda ya kamata na nema domin na yi bincike na, kuma na yi musu tambayoyi, ba wani na sa ya yi min ba.
“Sanadiyyar wannan bincike da na rika zuwa da kuma tambayoyin da na rika yi wa mutanen da ban taba tsammani zan hadu da su a rayuwa ta ba, haka ya kara min sani kuma ya sa na san wasu abubuwa sosai da a da ban san su ba, kuma ban san cewa ban san su ba din ba.” Inji Obasanjo.
Obasanjo ya kira da a kara kudade wajen tafiyar da tsarin NOUN a kasar nan.
A karshe ya godewa jami’ar NOUN, kuma ya yi alkawarin yin alfani da ilmin da ya samu wajen kara habbaka Najieriya.
Shi ma Gwamnan Bayelsa, Dickson, ya bayyana yadda Obasanjo ya burge shi, har ya nuna cewa tabbas NOUN ta burge shi, kuma idan ya kammala wa’adin sa, to zai koma karatu.
Da ya ke nasa jawabin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko a tarihin Nijeriya aka yaye dalibai mafi yawa, har 14,769.
Ya kara da cewa akwai dalibai na musamman wato Obasanjo da kuma Zaburidaya, wanda shi Zaburidaya, MBA ne ya yi.
Abdalla ya jinjina wa Obasanjo, wanda ya ce ya shiga karatun Ph.D ya na da sheakaru 80, ya kammala ya na da sheakru 82.
Daga nan sai ya kara yin nuni da abin da ya kira darasi a rayuwar Obasanjo, inda ya ce Obasanjo ya zama darasin da ke nuna cewa komin tsufan mutum, komin shekarun sa, to bai yi nisa da neman ilimi ba.
Farfesan ya nuna jero dimbin nasarorin da NOUN ta samu a cikin shekaru biyu da ya yi ya na shugabantar jami’ar.
Discussion about this post