Buhari ya bi gargadin muhaifina maimakon yi mini katsalandan – Iyabo Obasanjo

0

Diyar tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo, Sanata Iyabo Obasanjo, ta bayyana cewa abin kunya ne neman hada ta da mahaifinta da wasu a gwamnatin Buhari suke yi tun bayan mahaifin nata ya ja wa Buhari kunne cewa Kada ya kuskura ya ce zai sake fitowa takarar shugabancin kasar nan a 2019.

Iyabo ta ce kwakwulo tsohuwar wasikar ta da wasu a gwamnatin Buhari suka yi don su tozarta mahaifinta bai dace ba.

” Maimakon gwamnatin Buhari su maida hankali wajen yin hasashen abin da Obasanjo ya fadi a wasikar sa da yin juyayi Kan gazawar da gwamnatin sa ta yi sun buge da neman wanda za su dora wa laifi.

” Sun kwakwulo wata tsohuwar wasika ta suna ta yayadawa saboda su tozarta mahaifi na bayan ya gaya musu gaskiya ne.

” Bani da lokacin cika baki kan wutar da suke kokarin tadawa, shawara ta shine su bi gargadin da akayi musu, su hakura.

Tun bayan wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ga shugaba Buhari mutanen da yawa suke ta tofa albarkacin bakin su kan wasikar.

Wasu na ganin cewa Buhari ya bi shawarar da Obasanjo ya bashi na ya hakura da sake takara a 2019. Wasu kuma na ganin Obasanjo bashi da Imanin da zai yi wa Buhari wa’azi wai kada ya sake takara.

Share.

game da Author