Bayan wasikar gar-da-gar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba Muhammadu Buhari da ya jawo cece- kuce a kasa Najeriya, shugabannin biyu sun hade a kasar Ethiopia.
Shugabannin suna kasar Ethiopia ne domin halartar taron kasa da kasa na kungiyar hadin Kan kasashen Afrika (AU) dake gudana a Addis Ababa.
Bayan gaisawa da ya yi da sauran shugabannin kasashen Afrika ya nemi Buhari a cikin taro domin gaisawa dashi.
Manema Labarai sun yi ca kan shugabannin biyu a daidai suna gaisawa inda suka yi ta daukan su hotona ta ko ina.
Wasikar Obasanjo ga Buhari dai ya jawo cece-kuce tsakanin masoya gwamnatin Buhari da wadanda suke ganin Obasanjo mai gaskiya ne sannan abinda ya fadi gaskiya ce.