Buhari da kansa ya gargade mu kada mu ce komai game da wasikar Obasanjo

0

Wani na kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shugaba Buhari da kansa ya gargade su kada kowa ya kuskura ya ce zai maida wa tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo martini game da wasikar da ya rubuta masa.

Idan ba a manta Obasanjo ya rubuta wa Buhari wasika a makon da ya gabata cewa kada ya kuskura ya ce zai sake tsayawa takara a 2019, ganin cewa gwamnatin sa bata tabuka komai ba sannan shi kansa Buhari bashi da isasshen lafiya.

Hadimin Buhari ya kara da cewa ya gargadi duk wani ma’aikaci dake karkashin sa da ya iya wa bakin sa. Kada wani ya kuskura ya ce zai maida wa Obasanjo martini.

Ko dayake Jam’iyyar APC, da ministan yada labarai, Lai muhammed sun dan yi tsokaci kan wasikar, basu fadi wani abin suka ba ga Obasanjo.

Da aka tambayi hadimin game da martanin da Ministan sadarwa yayi wa Obasanjo, yace shi dai babu ruwan sa amma kuma ministan yayi don kan sa ne ba don wani ba.

Share.

game da Author