Boko Haram sun kashe mutane 5 a harin Adamawa

0

Mazaunan kauyen Kaya dake jihar Adamawa sun ce da safiyar ranar Juma’a wasu ‘yan Boko Haram sun kawo wa kauyen hari inda akalla mutane 5 suka rayukansu.

Wani mazaunan kauyen wanda ya tsira da ransa Baba David yace ‘yan Boko Haram din sun kawo harin ne da misalin karfe 10 na safe inda suka yi awowi 3 suna barin wuta.

Shugaban karamar hukumar Madagali Yusufu Muhammad ya tabbatar da wannan hari sai dai ya ce bashi adadin yawan mutanen da suka rasu.

Share.

game da Author