BOKO HARAM: Shekau na nan da rai, amma ya na fama da matsanancin ciwo

0

Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya na nan da rai, amma ya na fama da matsanancin ciwo. Haka su ka bayyana a ranar Litinin.

Sani Usman, wanda shi ne kakakin rundunar Sojin kasar nan, ya ce su na nan sun jajirce, nan da yan kwanaki kadan ba da dadewa ba za su kamo shugaban daya bangaren na Boko Haram, mai suna Abu Mus’ab Albarnawy.

“Ko tantama babu cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau na fama da matsanan cin ciwo, kuma ba ya iya tabuka komai. Ya zama kamar wani makahon doki, da ba ya iya hasala komai.

“Abu Mus’ab da ke ta yi wa matasa romon-kunne, ya na sa su a cikin dakarun sa, shi ma mun kusa kure ramin sa.

Saboda mun ji ya na nan ya na daukar yara ya na hure musu kunne.”

Kukasheka ya ce a yanzu kuma Boko Haram sun shigo da wata dabarar lullube saman rufin bukkokin su, ta yadda ba za a iya ganin hasken rufin dakunan ba, ballantana a kai musu hari ta sama.

“Haka nan gogarman nan Mamman Nur Algadi, shi ma an ji masa mummunan rauni, kusan ya ma gurgunce tun cikin 2014 a wani hari a Mubi, a lokacin da ya ke a kan babur.

Yanzu ba ya fita yaki, sai dai ya na koyarwa a sansanin Boko Haram, kuma ya na yin alkalanci.

Tare da wani mutumin Saminaka, mai su na Abu Mujahid aka ji musu mummunan rauni.

Amma shi Mujahid, Shekau ya kashe shi da kan sa.”

Share.

game da Author