Dan sanda Usman Hassan da rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ke masa zargin kashe wasu manoma 7 a gonar su dake karamar hukumar Gombi jihar Adamawa ya ce ‘yan Boko Haram ne ya kashe ba manoma ba kamar yadda ake zargin sa da aikatawa.
Ya ce yana da hujjojin da ya nuna cewa wadannan mutanen da ya kashe ‘yan Boko Haram ne.
A wata wasika da Hassan ya rubuta wa Sifeto-Janar din ‘yan sanda ya bayyana cewa tsohon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa Moses Jitoboh ne ya basu izinin bindige duk wani dan Bolo Haram da suka yi arangama da shi.
Hassan ya ce Jitiboh ya aiko masa da sako a watan Nuwamba cewa yana bukatan ya jagoranci ‘yan sanda don magance aiyukkan Boko Haram a wasu kauyukan dake karamar hukumar Gombi.
” Bayan na karbi wannan sakon sai muka tattauna da shi Jitoboh inda na fada masa cewa wannan aikin sojoji ne ba ‘yan sanda ba.”
” Ko dana fadi haka Jitobo dai ya dage kan bakar sa sannan ni kuma nace ina bukatan taimakon mafarautan wadannan wurare wanda shi Jitoboh ya amince da haka.”
” Nan da nan sai na aika wa shugaban mafarautan arewa maso gabashin kasar nan Mohammed Usman inda muka tattaunan yadda za mu fara aikin.”
Bayan haka Hassan yace a ranar 22 ga watan Nuwanba shi da ‘yan sanda tare da mafarauta suka fara wannan aiki inda suka yi kicibis da wasu da suke zargin ‘yan Boko Haram ne.
‘‘Mun zargesu ne da hakan ganin daga ganimu sai suka fara harbin mu sannan bayan mun sami nasarar harbe su ne na bada rahotan abin da ya faru wa Jitoboh.”
“Jitoboh na samun wannan rahoton da na aika sai komai ya daburce ya sa aka kama ni tare da ‘yan sandan da na yi aiki da su da kuma mafarautan.”
Hassan ya kuma ce wasu ‘yan Boko Haram din da ya kama tare da masu siyar da miyagun kwayoyi duk an sake su batare da an kai su kotu ba. Sannan ya ce wasu ‘yan Boko Haram din na biyan kwamishinan cin hancin miliyoyin naira don ya sake su.
Lauyan dake kare Hassan, Femi Motojesi, wanda ya bada wannan rubutacciyar korafi wa manema labarai ya yi kira ga Sefeto-Janar na ‘yan sanda da ya gudanar da binciken wannan magana domin maganar ta fi karfin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa.
Manema labarai sun ce sun kasa samun shi tsohon kwamishinan ‘yan sanda Moses Jitoboh amma sun yi magana da shi sabon kwamishinan wato Abdullahi Yerima inda ya tabbatar da cewa sun kama Hassan sannan suna yin bincike akan sa.