BINCIKE: Sojoji da ‘yan sanda sun fi kamuwa da Kanjamau a Najeriya

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau na kasa, NACA, Sani Aliyu ya ce binciken hukumar ‘Integrated Biological and Behavioural Surveillance Survey’ ya nuna cewa sojoji da ‘yan sanda na cikin kungiyoyi 6 da suka fi kamuwa da cutar kanjamau a kasar nan.

Ya sanar da haka ne da ya ke gabatar da jawabin sa a taron kiwon lafiya wanda ma’aikatar tsaro ta shirya a Abuja.

Ya ce bincike ya nuna cewa a shekarar 2017 jami’an tsaro 220,000 ne suka kamu da cutar kanjamu a kasar nan.

Daga karshe Aliyu ya ce bisa ga bincike, direbobi da kwandastocin mota, karuwai, masu yin luwadi, suna cikin wadanda suka fi kamuwa da cutar kanjamau a kasar nan.

Share.

game da Author