BAKON DAURO: Za a yi wa yara sama da miliyan 1 rigakafi a Jihar Neja

0

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa za ta yi wa yara miliyan 1.4 ‘yan kasa da shekara biyar alluran rigakafin cutar bakon dauro a jihar.

Jami’in hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Mohammed Usman na ya fitar da wannan sanarwa ranara Alhamis da yake ganawa da manema labarai a Minna.

Ya ce za a fara yin allurar ne daga ranar 8 zuwa 26 ga watan Faburairu.

Daga karshe Usman ya yi kira ga iyaye da su yi kokarrin anyi wa ya’yan su allurar.

Share.

game da Author