Hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko reshen Abuja ta kammala shiri tsaf domin yi wa yara allurar rigakafin cutar bakon dauro.
Shugaban hukumar Mathew Ashikeni ne ya sanara da haka a hira da yayi da kamfanin dillancin labarai.
Ya ce sun tsara shirin ne yadda za su iya yi wa yara ‘yan watanni 9 zuwa shekara 5 alluran rigakafin daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Fabrilu 2018
Ashikeni ya kuma ce iyaye za su sami yi wa yaran su rigakafin ne a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake usa dasu, a makarantu, bakin tituna dasauran su.
Daga karshe yayi kira ga iyaye da su mara wa shirin baya wajen fitowa da ‘ya’yan su ayi musu wannan allura.