Babu abin da Buhari ya tsinana wa Najeriya, ba zan yi shi ba – Ghali Na’abba

0

Tsohon kakakin majalisar Wakilai, kuma jigo a jam’iyyar APC Ghali Umar Na’abba ya nuna fushin karara ga yadda Buhari ya ke gudanar da mulki a kasar nan.

Ghali ya ce tsautsayi ne ya sa ya mara wa Buhari a 2015,ko da yake ya ce yana ganin kamar a wancan lokacin Buhari zai kawo kyawawan sauyi ne ga siyasar Najeriya, sai gashi abin sai kara tabarbarewa yayi.

” Na taba zama da shugaban kasa, na gaya masa cewa gaskiya fa akwai matsala a kasar nan, amma cewa yayi dama can akwai wadannan matsaloli tun kafin ya zamo shugaban kasa, amma yanzu tunda an zabe shi komai zai gyaru. Abin da ya fadi ya dade yana min ciwo a zuciya. Babu wani abu da yayi na inganta demokradiyya a kasar nan, saboda haka babu abin da zai sa in sake mara masa baya koda ya fito takara.

” Daga kalaman sa a wancan lokacin, na ga kamar zai zo ya gyara demkradiyya a Najeriya ne, sai gashi abin ba haka bane. Shekaru uku kenan bayan hawan sa shugaban kasa. Baya aiki da jam’iyya sannan yana ganin duk wani dan jam’iyya makiri ne ko ko ba mai gaskiya bane sannan ba ya neman shawaran ‘yan jam’iyya kan komai.

Da aka tambayeshi ko jam’iyyar APC za ta fitar da wani dan takarar shugaban kasa banda Buhari, Ghali ya ce ” Ay wasu sun nannade jam’iyyar sun saka ta a ajjihu, sai yadda suke so, sune suke ta sanarwa wai sun tsayar dashi Buhari dan takaran jam’iyyar ba tare da sun tuntubi kowa ba.

Share.

game da Author