Shugabannin al’umma da ‘yan siyasar jihar Benuwai sun sanar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa basu da filin da za su iya ba gwamnatin tarayya don kirkiro da yankunan kiyo a jihar da akayi wa suna ‘Colonies’.
Wadanda suka gana da Buhari a fadar gwamnati sun hada da gwamnan jihar, Ortom, David Mark, George Akuma da sauran su.
Sun ce idan wasu jihohin na da irin wadannan filaye, su ba su da shi.