Ba Fulanin Najeriya ba ne ke kai mana hari – Inji Sarakunan Filato

0

Wasu Sarakunan gargajiyar jihar Filato, sun yi zargin cewa Fulani makiyayan da ke kai musu hari, ba Fulanin cikin kasar nan da suke zaman lafiya tun fil azal da su ba ne.

Wadannan sarakunan gargajiya sun yi wannan jawabin ne sun yi wannan jawabi ne, a wurin wani taron neman wanzar da zaman lafiya a jihar, wanda rundunar ’yan sandan jihar ta shirya.

An gudanar da wannan taro ne a na shugabannin gargajiya, shugabannin jama’a, shugabannin addinai daga kananan hukumomin Riyom, Bassa, Barkin Ladi da kuma Jos ta Kudu.

Patrick Mandong, shi ne basaraken da ke rike da sarautar Gomre na Kuru ta cikin karamar hukumar Jos ta Kudu, ya ce akwai ambaliyar shigowar bakin Fulani makiyayya daga kasashen ketare da ya ce sun yi kaka-gida a masarautar sa, kuma ya ce barazana ce sosai a gare su.

“Fulani makiyayan da ke kai mana hare-hare bakin Fulani ne daga waje, ba Fulanin da muke tare da su a na nan kasar, shekara da shekaru mu na zaman lafiya da su babu tsangwamar juna.

“Misali, idan a yanzu haka ka je masarauta ta, za ka ga su bakin Fulanin a bayan Kwalejin Makarantar ‘Yan Sanda sun yi dafifi. Amma da ka matsa musu da tambayar ko daga ina suke, sai ka ji sun ce maka ba su son a cika su da tambayar kwakwaf.” Inji Basaraken.

Shi kuma Braa na al’ummar Iregwe, Ronku Akaa, cewa ya yi al’ummar sa na zaune lafiya da Fulani makiyayan da ke yankin sa shekaru masu yawan gaske. Amma ba a fara kai musu hari ba, sai bayan da Fulanin suka bar yankin na sa.

“Amma makiyayan da ke kai mana hari sun a cinye mana amfanin gona da kona mana gidaje, ba Fulanin da mu ka sani mun yi rayuwar arziki da su na nan cikin kasar mu ba ne.

“Amma dai ganin yadda zan ake kai mana hari, zan iya cewa ‘’da-dan-gari-a-kan-ci-gari.”

Share.

game da Author