AUREN SHEKARA 22: Kotu ta raba saboda mata ta ki daina sa Wando

0

Auren wata mata mai suna Fatimot Abiola ya mutu a yau Laraba, bayan ta shafe shekaru 22 tare da mijin ta Rasheed, a bisa dalilin ta na tsuke da dogon wando, alhalin mijin ya yi mata hani da hakan.

Rasheed da Fatimot sun shafe shekaru 22 su na tare.

Alkalin kotun gargajiya ta Iyando da ke Lagos, Akin Akinyini, ya bayyana cewa, a yadda ya fahimci abin dai kawai ma’auratan sun gaji da juna ne kawai, domin duk wani kokarin a sasanta su, ya ci tura.

Tun da farko sai da Rasheed ya shaida wa kotun cewa matar sa Fatimot ta kan tsuke da dogon wando ta shiga gari yawo, alhali ya yi mata gargadin kada ta sake ta saka wandon.

“Ba ni kadai ba ma, hatta mahaifiyata ta sha gargadin ta cewa ta daina saka dogon wando, amma ba ta daina ba, don haka ni dai ba zan iya jure irin salon sabuwar rayuwar da ta dauka ba.”

Rasheed mai shekaru 47, jami’in kwastan ne, wanda kuma ya kara da cewa matar sa na yi barazanar kada ya sake ya kara aure.
“Amma kuma ni da Fatima mun shafe shekaru ba mu yi kwanciyar aure ba.” Inji Rasheed.

“Akwai lokacin da ta fice daga gida na, ta shiga duniya, sai da ta shekara daya cur kafin ta dawo.

Sai dai ita Fatimot, ta ce mijin ta na cewa wai shigar karuwanci ne sa wandon da ta ke yi, kuma ita ba ta taba hana shi kara aure ba.

Akwai ‘ya’ya uku a tsakanin ma’auratan kafin kotu ta raba auren.

Share.

game da Author