Allah ya ba askarawan Najeriya sa’an dakile wata hari da da zai iya sanadiyyar rasa rayukan daruruwan mutane a garin Gamboru Ngala, dake jihar Barno.
Askarawan sun sami nasarar haka ne bayan hana wasu ‘yan mata uku da suka doso hanyar shiga garin duk sun yi jigida da bamabamai.
A bayanan nasarar da askarawan suka yi wanda Janar Sani Usman ya saka a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa tun bayan hango su da askarawan suka yi
sun yi kokarin dakatar da su kafin su aikata wannan mummunar aiki, sannan suka kwance bamabaman dake daure a kugun ‘yan matan.
Ita na uku daga cikin su ta boye nata ne a wajen gari, sai dai bayan tursasa ta da aka yi ta kai sojojin inda ta boye.
A hotunan da aka saki, Jama’an gari dai sun yi cincirundo a can da nesa suna gani wa kan su ikon Allah.
Yanzu dai an tafi da yaran domin ci gaba gudanar da binciken akan su.