Jam’iyya mai mulki, APC ta yi zankaleliyar kamu a jihar Kano, jiya Asabar.
Fitacce, kuma gogan Dan siyasar nan Basheer Lado Wanda aka fi sani da ‘mai kayan miya’ ne ya wancakalar da jam’iyyar sa ta PDP ya canza sheka zuwa APC tare da magoya bayan sa 5000.
A gagarumin bukin da akayi a Kano na tarban Lado, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce a lokacin Lado na Sanata ne ya matsa aka ba da kwangilar gina gadar sama na Zariya road dake Kano, sannan shine ya yi dalilin bada kwangilar titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Abuja.
Jiga-jigan jam’iyyar APC na jiha da kasa ne suka halarci taron yi wa Lado lale-lale maraba da zuwa jam’iyyar APC.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa Segundo Oni, Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa Maso Yamma, Inuwa Abdulkadir, Osita Izinaso, Ita Enang, Rabi Abdullahi duk sun halarci taron.
Gwamnonin da suka halarci bukin karbar Lado sun hada da gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, Adamawa Jibirilla Bindow, Sanatoci da sauran manyan ‘yan siyasa.