Kotun a garin Masaka jihar Nasarawa ta daure wani dalibi dan shekara 21 mai suna Antony na tsawon watanni 9 saboda kamashi da laifin satan kwalban manja daya da mudun wake 62.
Lauyan da ya shigar da karan a kotu Frank Swem ya ce Ibrahim Christiana da Benjamin Uzor makwabtan Anthony ne da ke zama gidan haya tare da shi ne suka kai karar abin da ya aikata ofishin ‘yan sandan dake Masaka ranar 5 ga watan Janairu.
” Masu kara sun ce Anthony ya sace kwalban manjan ne da mudun wake 62 dake daure a dakin su da yamma ranar 6 ga watannan.”
Daga farko Alkalin kotun Yakubu Ishaku ya yanke hukuncin daure Anthony na tsawon watani 9 ne, sai bayan Anthony ya roki sassauci sai alkali Ishaku ya ci shi taran Naira 10,000 ko zaman gidan wakafi har na wata 9.