Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da sace ‘ya’yan dan majalisar wakilai, Yahaya Chado, dake wakiltan Maradun da Bakure.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Mohammed Shehu ya sanar da haka wa manema labarai jiya litini a garin Gusau. Sannan ya kara da cewa masu garkuwan sun sace yaran ne a gidan mahaifinsun dake kauyen Gora a karamar hukumar Maradun da misalin karfe daya na dare.
Wani mazaunin kauyen Kabiru Mai-Kwashe ya fada wa manema labarai cewa barayin sun zo gidan dan majalisan a kan babur dauke da bindigogi suka dauke Muhammad Yahaya mai shekara 27 da wansa Junaidu Yahaya mai shekara 35.
” Yayin da barayin ke kokarin shiga gidan ne suka ji wa mutane 4 rauni sannan sun kashe wasu mutane.”
Discussion about this post