Rundunar ’Yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace wasu Ba’Amurkawa biyu da ‘yan kasar Canada biyu, bayan an kashe jami’an ‘yan sanda biyu kafin a gudu da su.
Kakakin rundunar, Mukhtar Aliyu, ya tabbatar da haka, a yau Laraba, inda ya kara da cewa an kashe ’yan sandan biyu ne a kokarin su na kwato Turawan.
An sace su ne a Kagarko, kan titin Abuja zuwa Kaduna a jiya Talata da dare, a kan hanyar su ta zuwa Abuja daga Kaduna, da misalin karfe 8 na dare.
Ya ce zaratan ’yan sanda na can na kokarin bin sawun wadanda su ka yi garkuwa da su.
Discussion about this post