Wata Kungiyar Rajin Kare Hakkin Dan Adam, mai suna ‘Access to Justice, ta rubuta takardar korafi ga Majalisar Dinkin Duniya, dangane da ci gaba da tsare Sheik Ibrahim El-Zakzaky da ake yi a Najeriya.
A cikin wata wasika da kungiyar ta tura wa Diego Garcia-Sayan, wanda shi ne jami’in tuntubar Hukumar Lauyoyi da Alkalai Masu Zaman Kansu, kungiyar ta yi nuni da irin yadda gwamnatin Nijeriya ta yi fatali da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta zartas inda ta bayar da umarnin a saki El-Zakzaky.
Mataimakin Daraktan kungiyar mai suna Adenike Aiyegun ne ya sanya wa takardar hannu a ranar 14 Ga Janairu, 2018.
“Irin yadda gwamnatin Buhari ke nuna rashin bai wa kowane bangare na gwamnati hakkin sa a cin gashin kai, ta hanyar take doka, to ya na fa kawo barazana ga amantakewa da ma dorewar dimokradiyya a kasar nan. Sannan kuma irin wanna karfa-karfa ta sa an rigaya an dawo daga rakiyar gwamnatin saboda halayyar ta wajen take umarnin kotu.
“Baya gannan kuma, gwamnatin na kara rura wutar fadan kabilanci da addinanci a cikin kasar, wanda idan ba a gaggauta daukar matakai ba, to tabbas zai kawo barkewar mummunan rikici. A matsayin ta na mamba a kungiyar Majalisar Dinkin Duniya, tilas ne a tilasta Nijeriya bin ka’idoji da sharuddan da majalisar ta gindaya.
Ana tsare da El-Zakzaky ne shi da matar sa tun cikin Disamba, 2015, sayan harin da aka kai gidan sa da kan mabiyansa, wanda aka she mabiyan sa 47.
Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a sake shi tun cikin Disamba, 2016, amma gwamnatin tarayya ta yi biris da wannan hukunci na kotu. Gwamnati ta ce ana tsare da malamin ne domin haka ne mafi a’ala kan rayuwar sa.
Kungiyar ta ci gaba da cewa wannan karan-tsaye da gwamanti ta yi wajen take umarnin kotu, ya sa sauran hukumomin tsaron na gwamnati su ma sun fara bin baya ko kwaikwayon ta wajen take hakkin ‘yan Nijeriya ba tare an tsawata musu ba.
Ya buga misalign cewa a yanzu haka akwai mabiyan malamin har 52 da aka kama a Abuja wurin zanga-zangar lumana da suka gabatar a Abuja a karshen makon da ya gabata.