An Kaddamar da sabuwar kungiyar Obasanjo a Abuja

0

Yau Laraba ne ake Kaddamar da sabuwar Kungiyar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kirkiro mai suna ‘Coalition for Nigeria’ yau a dakin taro na gidan Shehu Musa ‘YarAdua’, Abuja.

Idan ba a manta ba, Obasanjo ya sanar da kirkiro da wannan kungiya ne a wasikar sa da ya rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na kira garesa da kada ya nemi tsayawa takara a 2019.

Tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola, wanda shine yake shugabantar kungiyar, yace wannan kungiya ba tariga ta zamo jam’iyya ba tukuna.

” Idan muka gama haduwa sannan muka ga ya dace muyi mata rijista domin ta zamo jam’iyya zamu yi. Amma yanzu kam muna nan a matsayin Kungiya.”

Gwamnoni 10 da tsoffin da ‘yan siyasar kasar nan duk sun nuna goyon bayan su ga kafa wannan kungiya.

Share.

game da Author