Gwamnatin Tarayya ta fara binciken wasu sabbin rahotannin hura usur da ke da alaka da harkallar kudade har wurare 200.
Ministar Harkokin Kudade, Femi Adeosun ce ta bayyana haka, ta na mai karin cewa wadannan harkalloli ne na dakile yawa ko adadin kudadenn da suka kamata a biya a matsayin haraji ga gwamnatin tarayya.
Sai kuma yadda malaman tara kudaden haraji ke hada baki da jama’a ana ba su toshiyar baki, su kuma su na zabtare yawan kudin da mai biyan haraji ya kamata ya rika biya.
Ministar ta ce a kan haka kuma za a sake bullo da wata sabuwar dabara tara kudaden haraji tare da tantane jami’an jabu daga masu tara haraji na kwarai.
Kemi ta yi wannan bayani ne a ranar Lahadi a Abuja, yayin da ta ke taro da Shashen Kula da Hura Usur na Ma’aaikatar Kudade ta Tarayya tare da Kwamitin Ofishin Shugaban Kasa Mai Kula da Binciken Kudade.
Ta ce ana kara tsaftace hanyar tara kudaden harajin ne tare kuma da yin la’akari da kara zaburar da jama’a muhimmanci da wajibcin biyan haraji da wannan gwamnati ta dauka da muhimmancin gaske.