An ceto ‘yan Amurka da Kanada da aka sace a Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da ceto ‘yan Amurka da Kanada hudu da aka yi garkuwa dasu a Titin Kaduna-Kagarko- Abuja a makon da ya gabata.

Kakakin rundunar’yan sandan jihar Mukhtar Aliyu ya ce an samu nasarar ceto su batare da an biya kudin fansa ba.

Ya ce jami’an ‘yan sandan sun fantsama dazukan yankin inda Allah ya basu nasarar ceto mutanen.

Share.

game da Author