Allah ya yi min isharar tsayawa takarar shugaban kasa – Tunde Bakare

0

Babban Limamin Cocin Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya bayyana cewa Allah ya yi masa ishara da ya tsaya takarar shugabancin kasa.

Bakare dai ya tsaya takara tare da Shugaba Muhammadu Buhari, a zaben 2011, a matsayin mataimakin shugaban kasa, amma ba su yi nasara ba a lokacin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Bakare ya shaida wa dubun bubatar mahalarta yayin taron sabuwar shekara cewa Allah ya yi masa isharar tsayawa takara, cewa kada ya i watsi da muradin sa na siyasa, amma bai yi masa nuni da shekarar da zai tsaya takarar ba.

“Wannan isharar da zan sanar da ku mai wahalar bayyanawa ce, amma dai na san idan na bayyana wasu za su yi murna, wasu kuma su yi ta suka ta. Saboda ko na ce zan danne a zuciya ta, tsarkin ruhi ba zai bar ni na ci gaba da dannewa ba.

“Ina cikin halwa wajen asubahin daren Lahadi, sai Allah ya yi min ishara da cewa, kada na daina siyasa, domin akwai haske a gaba. Ya ce na fito takarar shuagaban kasa. To amma zan yi wannan takara a lokacin da ya ke daidai.

Ya kara da cewa ya san abu ne mai wahala hakar sa ta cimma ruwa, to amma tunda Allah ne ya ce ya yi takarar, zai fito a lokacin da ya dace ya fito, saura kuma sai ya bar wa Allah zabin mafi alhairi tsakanin yin nasara ko faduwa zabe.

Bakare ya ce komai na Allah ne, har ya buga misali da Annabi Yusuf A.S, wanda bai taba ma tsayawa takara ba, amma ya zama shugaban Misira.

“Idan ba ku manta ba, cikin 1998, na shaida muku cewa wani shugaban kasa zai mutu a tsakiyar mata biyu. Shin hakan ya faru ko bai faru ba?

“Yanzu ma ina kara shaida muku cewa wasu gaggan ‘yan siyasa za su riga rana faduwa sakamakon leke-leken fatarin mata da suke yi. Za ku gani, ni na fada muku.” Inji Bakare.

Share.

game da Author