Babban Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya gargadi ‘yan jarida da kafafen yada labarai masu yi wa shari’a katsalandan su na tattauna batutuwan da ke kotu wadanda ba a kai ga yanke hukunci a kan su ba.
Ya furta hakan ne a cikin wani jawabin marhabin da shigowar Sabuwar Shekara da ya yi wa ’yan jarida a jiya Talata.
Ya yi bayanin ne ta hannnun jami’in hulda da ‘yan jarida na Babban Alkalin, mai suna Awassam Bassey.
Jawabin ya nuna cewa su kan su lauyoyi sun afka cikin irin wannan haramtaccen katsalandan din su na bayyana ra’ayoyin su a fili kan wadansu shari’un da ke a gaban kotu.
Daga nan sai ya tunatar da duk masu yin irin wannan katsalandan din cewa su na fa sane da cewa akwai dokar da ta yi tanadin hukuncin da ya hada har da dauri a kan duk wanda ya shigar wa kotu hanci da kudundune.
“Haram ne ga duk wani lauya ko jarida su rika yada wani ra’ayi na sukan wata shari’ar da ta danganci aikata laifuka wadda ke a gaban kotu. Kai, ko da an rigaya an yanke hukunci ne, amma wani bangare ya daukaka kara, to haram ne a rika yada ra’ayoyin fahimtar wani a kan wannan kara ko shari’a.”
“Ba za mu zura ido mu na kallo ana yanke hukuncin wata kara ko shari’a a shafukan jarida tun kafin kotu ta bayyana mai laifi da mai gaskiya ba.’’ Inji Onnaghen.
Discussion about this post