Akawo mana dauki, Almajirai sun addabe mu a Adamawa – Kungiyar Musulmai

0

Kungiyar Musulmai a jihar Adamawa ta koka da yadda Almajirai ke shigowa manyan garuruwan jihar kamar kiyashi.

Kungiyar tayi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kawo wa jihar dauki domin abin ya wuce misali. Sannan ta yi kira ga iyaye da su ji tsoron Allah su kula da ‘ya’yan su a gidajen su, su basu ilimin addini yadda ya kamata ba kawai su turo su garuruwa ba suna ta gararamba a manyan tituna.

“Duk inda kabi a manyan garuruwan Adamawa zaka gansu kamar kiyashi suna barace-barace.”

Takardar wannan shela ya fito ne daga kwamitin kungiyar musulmai na jihar Adamawa da Gambo Jika da Abdullahi Damare suka sanya wa hannu.

Share.

game da Author