Kungiya mai zaman kanta na kare hakin yara ‘Child Protection Network CPN’ ta bukaci rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta binciki shugaban cibiyar kula da yara ‘yan gudun hijira ‘Stephen Children Centre’ Isaac Newton-Wusu.
Kungiyar ta shigar da karan ne a ranar 9 ga watan Janairu inda ta zargi Isaac da aikata fyade da azabtar da yara ‘yan mata dake zama a wajen musamman ‘yan mata ‘yan gudun hijira daga yankin arewa maso gabashin kasar nan.
Kungiyar ta ce tana bukatan gwamnati ta karbi kula da aiyukkan wannan wuri daga hannun Isaac har sai an kammala binciken zargin da ake masa.
Kungiyar ta ce ta shigar da wannan kara ne bisa ga koken haka da suka samu daga wajen wasu ‘yan mata biyu da suka zauna a wajen sannan da tabbacin aikata haka da sakamakon binciken da suka yi.
Daga karshe Isaac ya musanta wannan zargi da aka yi masa sannan ya kara da cewa anyi haka ne domin a kwace kula da yaran daga cibiyar ta sa.