2019: Matasan Daura za su siya wa Buhari fom din takara

0

Kungiyar matasa dake garin Daura mai suna ‘Daura Emirate Youth Progressive Movement’ DEYPM, ta ce za ta siya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari fom din zarcewa.

Shugaban kungiyar Abdulkadir Lawal, ya ce matasan sun yi haka ne domin ba shugaban kasa da gwamnan jihar dama a karo na biyu su ci gaba da ayyukan alheri da suke yi a kasa Najeriya.

Matasan masarautar Daura da ya hada da Daura, Baure, Zango, Mai’adua and Sandamu sun yaba wa shugaban kasa kan nasarorin da gwamnatin sa ta samu a tsawon shekarun da tayi tana mulki zuwa yanzu.

Share.

game da Author