2019: Majalisar Wakilai ta sauya ranakun zabe

0

Majalisar Tarayya ta sasauya jadawalin ranakun zabukan 2019, wanda Hukumar Zabr Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC ta fitar makon da ya gabata.

Wannan sauye-sauye da majalisa ta yi, ya nuna a yanzu za a fara yin zaben Majalisar Tarayya ne, daga nan kuma sai na gwamnoni tare da na majalisar jihohi daga nan kuma sai na shugaban kasa ya kasance shi ne a karshe.

Kwamitin ‘yan Majalisar Tarayya ne wanda Mataimakin Kakakin Majalisa, Yussuf Lasun ke jagoranta ya yi wannan sauye-sauyen ranakun.

Sun bayyana cewa sun yi wadannan sauye-sauyen ranakun ne bisa ga la’akari da rahoton da kwamitin harkokin zabe ya gabatar, na bukatar a yi wa dokar zabe ta 2010 kwaskwarima.

A wannan jadawalin ranakun zabe da INEC ta fitar daga farko, ya nuna cewa zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya ne za a fara yi, kamar yadda aka yi 2015, sannan na gwamnoni da majalisaun jihohi ya biyo baya.

Share.

game da Author