2019: Lakanoni 10 da BUHARI zai yi ya ci Zabe

0

Nan da watanni kadan Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta cika shekara uku da kafawa.

Sannan kuma nan da watanni 13 za a sake zabe, domin a yi wa Najeriya sabon zubi, ko kuma a sake dafkara wadanda aka dafka a 2015. Ga wasu lakanoni 10 da Shugaba Muhammadu Buhari zai rubuce ya shanye, ko ya daura guru da layu da su, ya daura ko ya rataya, domin ya ci zaben 2019 PREMIUM TIMES HAUSA tayi muka nazari a Kai.

1- MATSALAR FETUR:

Ba a manta ba, tun daga watan Janairu, 2012 Buhari ya shiga sahun gaban masu sukar gwamnatin Goodluck Jonathan, su na cewa ta bari ana sace kudin Najeriya ta hanyar tallafin mai. Buhari ya ce ana shan fetur da tsada a naira 87.

Bayan ya hau kuma sai hikima da dabara ta subuce masa, har ya maida fetur naira 145, maimakon naira 45 da ya yi alkawari maida shi idan ya hau mulki, a lokacin da ya ke kamfen.

A yau kuma gwamnatin Buhari ta sake shiga cikin halin-kaka-ni-ka-yi wajen matsalar man fetur. Duk da cewa ana saida lita daya a kan naira 145, akwai alamomin da ke nuna cewa babu makawa, nan gaba sai an kara kudin fetur.

Matsawar Buhari na so ya ci zabe, to ya sake dabarar gyara matatun man kasar nan tun kafin dare ya yi. idan kuwa ya kara kudin fetur, to talakawa za su kara dawowa daga rakiyar gwanatin sa.

MAGANCE YAWAN GARKUWA DA JAMA’A:

Cikin shekarun nan uku na mulkin Buhari, matsalar yin garkuwa da jama’a ta yi muni kwarai. A da tare hanya ake yi, a sace mutum. Yanzu kuma abin ya kara muni, ta yadda ta kai har gida ake zuwa a buga wa mutum kofa, ya bude, a yi gaba da shi. Bayan dan lokaci a rika kiran iyalan sa a na jinga ko cinikin adadin kudaden da za a biya a sako shi.

A kullum ana kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Amma abin da ke damun jama’a shi ne, na farko dai masu garkuwa da jama’a din nan sun ki karewa, sannan kuma har yau ba a jin labarin makomar wadanda ake kamawa.

Shin kashe su ake yi? Ana kai shu kotu ana shari’a? Ana yanke musu hukuncin kisa ne ko kuma daurin rai-da-rai? Shiru ka ke ji, sai dai a rika cika soshiyal midiya da hotunan wadanda aka kama.

MAGANCE RIKICIN MAKIYAYA DA MANOMA:

Wannan matsala a halin yanzu ta fi muni a yankin Arewa ta Tsakiya, wato Middle Belta, domin can ne ke da albarkar wuraren kiwo, fiye da Arewa ta Gabas ko Arewa ta Yamma. Wannan matsala ta janyo wa Fulani bakin jini a kasar nan.

Yawanci idan Fulani sun yi kisa, to kisan daukar fansa ne suka yi. Akasarni jaridu ba su yayata kisan da ake yi wa Fulani da shanun su da ake sacewa ko ake kashewa.

Amma duk ranar da Fulani suka yi kisan daukar-fansa, to jaridu za su dauki kwanaki su na yayatawa, kuma ana aibata Fulani. Yawancin kabilu na jin haushin yadda Buhari ya kasa daukar kwakwkwaran matakin hana ruruwar rikicin a kullum.

Rikicin ya janyo wa gwamnatin sa bakin jini, haka zalika shi kan sa ya na fuskantar bakin jini a matsayin sa na Bafulatanin shugaban kasa wanda suke kallon ya zura ido, ya nade hannuwa ya bar Fulani ‘yan uwansa na kashe-kashe tsakanin su da makiyaya.

MAGANCE BARAYIN SHANU:

Su ma Fulanin, musamman na wasu yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara dagaruruwa na jin haushin gwamnatin Buhari, domin a cikin shekarun nan uku an karkashe su, inda barayin shanu sun sace musu dubban shanu bayan sun karkashe daruruwan su.

Wannan matsala ta faro ne musamman a Zamfara da Katsina da Birnin Gwari tun a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan. Dalili kenan a lokacin zaben 2015 aka yi wa Jonathan rubdugu, domin ana ganin idan Buhari ya hau, zai yi wa matsalar sha-yanzu-magani-yanzu. Amma har yau shiru ka ke ji. An kona garuruwa da kauyuka, an karkashe daruruwa, amma ko labarin tallafin a zo a gani ba a ji daga gwamnatin tarayya.

MAGANCE MATSALAR KIWON LAFIYA:

Idan aka yi nazarin alkawurran da APC ta yi a bangaren kiwon lafiya kafin ta hau mulki, za a ga cewa har yanzu fa akwai sauran sauran rina a kaba. Tun da Buhari ya hau gwamnati duk wasu bangarori na kiwon lafiya yajin aiki su ka shiga yi, kamar dama jira su ke yi Buhari ya au mulki.

Manya da kananan asibtoci na cikin halin jangwam. Babu wadatattun likitoci kuma har yau dai ko allura guda daya za a yi wa talaka, sai a ce masa “tafi kemis ka saya.” Duk tsananin ciwon mutum sai ya bata dodon lokaci kafin ya ga likita.

GYARA HARKOKIN NOMA:

A wannan gwamnatin, noma ne aka fi yayatawa a matsayin abin tinkahon da wannan gwamnatin ta ce ta inganta, baya ga dakile muggan hare-haren Boko Haram a cikin Arewacin kasar nan.

Amma har yanzu idan ka shiga cikin talakawa, za ka ji ana kuka daban-daban. Akwai masu cewa yawan takin zamanin da mai gona zai zuba, idan ya kwashe amfanin gonar zai ga cewa babu riba.

Sannan kuma a lokaci da ake noman a farkon damina har zuwa tsakiyar ta, amfanin noma na tsada. Amma da kaka ya na arha. Idan talaka zai sayar domin ya biya bukata, to sayar arha takyaf.

Sannan kuma Buhari zai hana shigo da shinkafa nan ba a dadewa ba cikin 2018, kamar yadda ya bayyana a cikin jawabin sa na sabuwar shekara. Ana kukan cewa tun da Buhari ya hau shinkafar waje ta yi tsada, kuma an kasa karya farashin ta. Akwai kuma masu cewa da wuaya a daina shigo da ita, domin dokar ba akan kowa za ta yi amfani ba.

Ana gudun za ta kara masifar tsada ne kawai idan an kafa dokar, a gefe daya kuma ba za a bada karfin yin amfani da ta nan gida ba. Misali, za a haramta wa shi kansa shugaba da sauran ma’aikatan gwamnati cin shinkafar gwamnati? Wadanne hanyoyi za a bi a inganta ta gida kuma a hana ta tsada kamar ta waje?

Har yau babu wani takamaimen kamfanin takin zamani a kasar nan. A shekarar 2017, duk girma da karfin tattalin arzikin Nijeriya, sai da ta hada kai da kasar Morocco sannan aka samun takin da aka samu a kasar nan.

BATUN RUFE KAN IYAKA:

Matsawar Buhari ya tsananta rufe kan iyakoki, to zai fuskanci matsala, saboda har yau Nijeriya ta dogara ne wajen shigo da kusan komai, hatta reza da hankicin share majina da gumi, duk shigo da shi ake yi. Sau da yawa kuma rufe kan iyakokin kasar nan, kan shafi masu karamin karfi kawai.

TSANANTA HARAJI GA AL’UMMA:

Buhari da APC sun kafa gwamnati ne domin su samar wa jama’a rangwamen tsadar rayuwa da aka rika kuka da shi a gwamnatocin baya. Sai dai kuma alkalumman kididdiga sun tabbatar da cewa a zamanin mulkin APC an fi tsananta haraji kala-kala ga jama’a. kama daga jihohi da ita kanta gwamnatin tarayya, sun karfafa cewa za su rika samun kudaden shiga ne ta hanyar tilasta haraji.

Wannan matsala ta haraji na damun kananan ‘yan kasuwa wadanda ke kukan ba su samun riba sossai saboda karyewar darajar naira.

Akwai abubuwan more rayuwa da Buhari ya ce zai saukaka wa al’umma anmma a yau an karke ana shan su da tsada, musamman wutar lantarki da fetur. Bugu da kari, ya kamata Buhari ya sani cewa yawan korar ma’aikata da wasu gwamnonin sa key i, to fa tabbas tamkar ana korar masu jefa kuri’a ne zuwa wata jam’iyya daban.

N-POWER:

Ana jinjina wa gwamnatin Muhammadu Buhari da ta bullo da shirin N-POWER.

Sai dai kuma ana ganin ba shiri ba ne da zai iya dorewa dindindin, haka kuma akasari matasa ‘yan boko ne da ba su samu aikin yi ko sana’ar dogaro da kai ba ne ke amfana da N-Power.

Shi kan sa N-Power din ana cin kwakwa kafin a samu, kuma yadda kae yawan yayata shirin da alfanun sa, bai kai gejin yawn masu amfana da shirin ba.

Ana kukan akwai dandazon milyoyin talakawa musamman a Arewa, wadanda suka sha rana da dukan ruwa akan goyon bayan Buhari, amma har yau ba su gani a kasa ba.

Don ka akwai gagarimin aikin samar da ayyukan yi.

HANA CIN HANCI DA RASHAWA:

Akwai bukatar Buhari ya yi da gaske wajen kakkabe cin hanci da rashawa.

Akwai batutuwa da ke kan teburin sa, wadanda ya kamata a ce wadanda suka aikata laifukan an gurfanar da su, amma shiru ka ke ji an ce ana bincike. Har yau talakawa na tambaya shin me ake yi da kudaden da ake kwatowa? Me ya sa har yau ba a daure ko da daya daga cikin daruruwan wadanda aka akama sun wawure dukiyar kasar nan ba?

Su fa game-garin talakawa na ganin cewa duk wani gyara idan ba a daure wadanda suka kassara kasr nan ba, to canji bai canzu ba daga 2015 zuwa 2019.

Share.

game da Author