2019: Buhari ya nada Amaechi darektan Kamfen din sa

0

A karo na biyu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi a matsayin darektan kamfen din sa a zaben 2019.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa Amaechi ya karbi wasikar nada shi daga fadar shugaban kasa kuma zai sanar wa duniya a mako mai zuwa.

Bayan haka kuma dan jarida Osasu Igbinedion ya tabbatar mana cewa lallai Amaechi ya riga ya dauki hirar da zai yi a faifai kuma za a saka a mako mai zuwa.

PREMIUM TIMES ta gudanar da bincike nata na musamman domin sanin tabbacin wannan rahota sannan ta gano cewa akwai kamshin gaskiya a maganar. Mun sami tabbacin cewa lallai haka ne akwai wannan shiri.

Da muka ne ta ji daga bakin kakakin Amaechi, David Iyofor, ya shaida mana cewa ba zai iya cewa ehhh ba, kuma ba zai ce a’a ba.

Ba tun a yau bane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke nuna alamun cewa zai fito takara a 2019. Ya fadi wani abu mai kama da haka da ya ziyar ci mutanen jihar Kano.

Share.

game da Author