2018: Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausan gargadi

0

Shugaban Majalisar Dunkin Duniya, Antonio Gutteres, ya yi kakkausan gargadi dangane da muhimmancin wanzar da zaman lafiya a 2018.

Da ya ke jawabin bankwana da 2017 tare da marhabin da zuwan 2018, Gutteres ya ce hakika 2017 da-baya-da-baya ta tafi, ba a samu wani ci gaban zaman lafiya a duniya ba.

Ya ce tun daga ranar da ya hau shugabancin Majalisar a 1 Ga Janairu, 2017, ya yi kira da a zauna lafiya a duniya. Amma maimakon haka, sai ma kara tirnikewa da rikice-rikice da kuma kashe-kashe kawai ya wanzu a fadin duniya.

“A cikin 2017 mun ga yawaitar masu zanzana su na karkarwar tayar da duniyar ta hanyar amfani da makamin nukiliya da sauran barazanar hana dan adam walwala, irin su take hakki.

“To za mu fuskanci matsalar canjin dumamar yanayi a duniya cikin 2018 da sauran kalubaken da zai shafi duniya baki daya. Mafita kawai ita ce mu kau daga tayar da fitintinu.

” Za mu iya daidaita junan mu ko sasanta tsakanin mu, ba tare da an dauki makami ba.”

A karshe ya yi fatan alheri ga duniya baki daya tare da addu’ar shigowar 2018 a cikin yalwa da dimbin alheran da ke cikin ta.

Share.

game da Author