Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula Da Kananan Yara, UNICEF, ta bayyana cewa a Nijeriya an haifi akalla jarirai 20,210 a ranar 1 Ga Janairu, 2018.
Wannan adadi da aka samu a Nijeriya, ya zo a matsayin na uku a cikin kasashen da aka fi yawan haihuwar jarirai a sabuwar shekara.
UNICEF ta ce akalla an haifi jarirai kusan 360,000 a ranar sabuwar shekara ta 2018, jiya Litinin kenan a duniya.
Hukumar ta kara da cewa kusan sama da rabin yawan wadannan jarirai da aka haifa a ranar 1 Ga Janairu, an haife su ne a kasashe tara kacal.
INDIA: 69,070
CHINA: 44,780
NIGERIA: 20,210
PAKISTAN: 14,910
INDONESIA: 13,370
AMURKA: 11,280
CONGO: 9,400
ETHIOPIA: 9,020
BANGLADESH: 8,370
Babban Jami’in Kula da Lafiya na Hukumar, Stefen Peterson, ya bayyana cewa duk da yawan hayayyafar da aka yi a ranar sabuwar shekara, akwai jarirai da yawa da ba su zo duniya da rai a ranar ba, wasu kuma sun mutu jim kadan bayan haihuwar su a ranar.