2017: An tarwatsa haramtattun matatun mai 500 a Bayelsa

0

Rundunar Tsaron Lafiyar Jama’a ta Civil Defence Corps, ta bayyana cewa a cikin shekarar 2017 ta tarwatsa tare da lalata haramrattun kananan matatun mai har guda 500 a jihar Bayelsa.

Kwamandan Hukumar Tsaron ne na jihar Bayelsa, Godwin Nwachukwu ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a ranar Laraba da ta gabata.

Ya ci gaba da cewa a cikin shekarar ta 2017, an sun samu nasarar cafke kananan kwalekwale har 60 wadanda akec safarar danyen man da suka sata da su. Ya ce tuni an lalata kwalekwalen dukkan su.

Godwin ya ce an kuma kama dukkan wadanda aka samu a cikin jiragen ruwan da aka samu su na jigilar danyen man da aka sata da su.

Sannan Shugaban na hukumar tsaron ya ce jiragen ruwa 60 da aka kama a cikin shekara daya, an same su da jimillar litar danyen man fetur har sama da lita milyan 50.

Share.

game da Author