Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa shirme ne kace wai PDP ba za ta sake yin Mulki a kasar nan ba wai don Kada da ita da APC tayi a Zaben 2015.
Atiku ya fadi haka ne da ya ke tattaunawa da amsa tambayoyin mutane a shafin sa na sadarwa ta yanar gizo bayan ya sanar da komawa jam’iyyar PDP.
Ministan yada Labarai, Lai Mohammed a wata ziyara da ya kai jihar Jigawa ya ce jam’iyyar PDP ba za ta sake cin Zabe a kasar nan ba.
Atiku ya ce rashin kangado mutum ya ce haka.
Atiku ya canza Sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a makon da ya gabata.