ZARGIN DALA BILYAN DAYA: “Da amincewar Gwamnonin PDP za a kashe kudin, inji APC

0

Jam’iyyar APC ta maida wa PDP raddi dangane da zargin da ta yi cewa Gwamnatin Buhari za ta fitar da Dala biliyan daya, don amfani da su ga yakin neman zaben 2019, amma ba son yaki da Boko Haram ba.

APC ta ce zargin da PDP ta yi ya nuna cewa jam’iyyar ba ta yarda da nagartar gwamnonin ta ba ma kenan.

Cikin makon da ya gabata ne dai gwamnonin kasar nan suka ce sun amince wa Gwamnatin Tarayya ta cire kudi daga Asusun Rarar Fetur har Dala Bilyan daya domin a sayo makaman yaki da Boko Haram.

Wannan furuci ya janyo wa Gwamnatin Buhari caccaka kama daga masu adawa da sauran jama’a.

Idan ba a manta ba, Buhari da mukarraban sa sun sha bayyana cewa an murkushe Boko Haram. Dalili kenan wasu ke cewa to don me za a fitar da naira biliyan 1 a ce za a sayo makaman yaki da Boko Haram kuma?

Shi kuwa Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, nan da nan ya fito ya ce za a cire kudin ne kawai don APC ta kashe wajen kamfen a 2019.

APC ta goranta wa PDP cewa ai ita ce ma jam’iyyar da ta kashe kudin makamai ga zaben 2015. Ta buga misali da wasu kudi Dala biliyan biyu da gwamnonin lokacin suka amince wa Gwamnatin Jonathan ta cire ana gab da zaben 2015.

Share.

game da Author