An wayi gari yau ana zaman dar-dar a garin Numan da wasu kauyuka dake kewaye da garin sanadiyyar kashe wasu ‘yan sanda 6 da kayi a kauyen Dowaya.
Wasu da suka tsokata wa PREMIUM TIMES sun ce Fulani ne da suka yi kaura daga kauyukan su da aka kai musu hari kwanakin baya suka koma garin Dowaye suna zamammakoki da addu’ar cika kwanaki arba-in da yi wa ‘yan uwan su kisan gilla da ake zargin ‘yan kabilar Bachama ne suka aikata, ‘yan sandan suka far ma.
Mazaunin ya ce Fulani na wannan zama ne sai suka ji wai ‘yan sanda suna hanyar su na kawo musu farmaki.Da suka zo sai rikici ya kaure bayan sun harbe wasu matasa biyu daga ciki fulanin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar, ya ce har yanzu suna tattara bayanai akan abin da ya faru domin shi bashi da cikakken bayani akai.
Yanzu dai an aika da karin jami’an tsaro kauyen domin gudun kada abin ya ci gaba haka sannan ana gudanar bincike akai.