Za a yi wa Trump gwajin lafiyar sa

0

Fadar Shugaban Amurka, White House, ta bayyana cewa za a yi wa Shugaba Donald Trump gwaji domin a tantance lafiya ko rashin lafiyar sa.

Kakakin yada labaran fadar ce, Sarah Sanders, ta bayyana haka a yau Juma’a.

Gwajin da za a yi wa Trump ya biyo bayan wata sarkewa da ya yi a ranar Laraba, yayin da ya ke jawabi a wani taro.

Sanders ta ce mutane na ta kara wa rashin lafiyar Trump gishiri, amma a gaskiya “makoshin sa ne kawai ya sarke.” Inji Sanders.

An ce a lokacin da ya ke jawabin, makoshin sa ya bushe, har ya yi ta kakarin kokarin furta kalmomi.

Za a yi masa gwajin ne a farkon shekarar 2018, kuma anbyi alkawarin cewa za a bayyana wa jama’a hakikanin abin da ke damun sa.

Trump, mai shekara 71 a duniya, shi ne shugaban Amurka wanda ya fi shekaru masu yawa a lokacin da ya ke kan zango na farko.

Cikin 2016, ya gabatar da bayanin lafiyar sa daga likitan sa. Sai dai kuma an yi kokari da shakkun sahihancin rahoton, saboda a sunkake aka bayyana shi, ba dalla-dalla ba.

Share.

game da Author