Za a tilasta gwajin kanjamau ga Ango da Amarya a jihar Kano

0

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta na kokarin kafa dokar gwajin cutar kanjamau ga ango da amarya a jihar.

Kwamishinan Kula da Lafiya na jihar, Kabiru Getso ne ya bayyana wa manema labarai haka a taron da aka shirya jiya Juma’a don ranar juyayin kanjamau ta dunya.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta dauki harkar kula da lafiya da muhimmmanci. Ya ce gwamnatin tare da hadin kai da Hukumar Hisbah ta jihar, sun tura wa Majalisar Jihar Kano da wani kudiri na neman a kafa dokar da za ta tilasta wa angwaye da amare yin gwajin cutar kanjamau tukunna.

Share.

game da Author