Shugaban hukumar NYSC Sule Kazaure ya ce gwamnatin tarayya na gab da kammala shirin saka dalibai masu bautan kasa cikin tsarin inshoran kiwon lafiya ta kasa NHIS.
Ya sanar da haka neda ya ziyarci sansanin jihar Osun ranar Alhamis.
” Na yi matukar farin ciki a lokain da aka sanar da ni ta wayar taraho cewa an kusa kammala shirin shigar da ’ya’ya na cikin tsarin inshoran kiwon lafiya ta kasa.”
Ya ce hukumar ta dade tana neman ayi hakan sai gashi Allah yayi komi ya kusa zama karshe.
Ya jinjina wa ‘yan bautar kasan da kuma kira gare su da su zama masu kishin kasa.
Discussion about this post