YANZU: Atiku da Makarfi na ganawar sirri

0

Ana can ana ganawar sirri tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Shugaban Riko na Jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

Ana wannan ganawar ce a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, a Wuse, Zone 5.

Atiku ya isa hedikwatar da misalin 12 na rana, yayin da dandazon magoya bayan sa suka isa wurin tun kafin zuwan sa.

Atiku ya fice daga APC ne ya koma PDP, kuma ana sa ran zai nemi tsaywa takarar shugabancin kasa ne a zaben 2019.

Share.

game da Author