A daidai ana shagulgulan bukin cikar Jihar Kaduna shekaru 100 da Kafuwa, daruruwan matasa dauke da muggan makamai suka Kai wa mazauna unguwar Badarawa, titin Katuru hari inda suka yi ta kwace wayoyin mutane suna sare-sare.
Jim kadan bayan wasu mazauna unguwar sun sanarwa ‘Yan sanda sai ko suka fatattaki wadannan yara sannan suka kama wasunsu da yawa.
Wani da akayi was kwace ya ce ya rasa wayar sa da kudin sa bayan kwace da suka yi masa a hanya.
Ya ce a gaban sa sun sari wasu mutane da yawa.
Abin dai bai yi wa ‘yan sharan dadi na domin ko ‘yan sanda Basu yi musu da dadi ba.