Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, ta bayyana cewa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da laifin kisan wasu dillalan shanu uku ‘yan Arewa.
Wadanda ake zargin dai ana tuhumar su ne da laifin kashe babban dillalin shanu Jibril Abdulkarim da kuma wasu yaran sa uku.
Kwamishinan ‘Yan sandan Bayelsa, Asuquo Amba, ya bayyana cewa ana ci gaba da binciken wadanda ake zargin tare da binciken wayoyin su domin a gane sakonni da kuma wayoyin da suke bugawa da wadanda suke mu’amala da su.
Kwamishinan ya yi wannan bayani ne a wata hira da shi da aka yi ta wayar tarho. Ya kara da cewa a irin kisan da aka yi wa Abdulkarim, akwai alamu da kuma zargin cewa lallai akwai kusanci ko sanayya a tsakanin wadanda suka yi kisan da kuma wanda aka kashe.
“Mu na kuma duba yiwuwar kisan ko ya na da alaka da zafin takarar shugabancin kungiya ta wadannan Fulani. Mu na fatan za mu samu kwakkwaran dalili da kuma tabbacin sauran wadanda ke da hannu a kisan.”
An kashe Abdulkarim da yaran sa uku ne a mayankar Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, a ranar 2 Ga Disamba.
Abdulkarim na da kusanci da gwamnatin jihar Bayelsa. Mamba ne ma na Kamitin Kula da Burtaloli da Dajin Kiwon Dabbobi na jihar, kuma shi ne Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Jihar Bayelsa.
Discussion about this post