‘Yan jarida ku daina yawan yayata aibin Najeriya -Sarkin Kano

0

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya Yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina haska wa duniya aibin Najeriya, maimakon haka, su rika aiki a bisa sharudda da kyakkyawan tafarkin ka’idojin aikin jarida.

Mai Martaba Sarki ya ce, “an wayi gari yanzu aikin jarida ya zama ‘inna-rididi”, wanda hakan kiyyayya ce kawai ya ke janyo wa kasar nan, ba wani ci gaba ba.

Ya kara da cewa ‘yan jarida su guji buga duk abin da zai zubar da kima da martabar Najeriya a duniya.

Sanusi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron kwanaki biyu ga masu ruwa da tsaki a aikin jarida, a Kano, wanda Kamfanin Tace Albarkatun Man Fetur, KRPC ya shirya a Kano.

Hakimin Dala, Alhaji Abdullahi Lamido Sanusi ne ya wakilci Sarki a wurin taron, kuma shi ne ya karanta jawabin sa. Ya na mai cewa yawan bada rahoton munanan abubuwan Nijeriya ya na yi wa kasar illa sosai.

” Abin da ya fi damu na shi ne yadda ku ‘yan jarida ke yawan yayata munanan rahotanni dangane da Nijeriya, abin da ba a cika ganin na wata kasar na yi wa kasashen su ba.”

Babban Daraktan kamfanin KRPC, Adewale Ladenegan, ya bayyana cewa akwai kalubale kan aikin jarida sosai a kasar nan.

Daga nan ya ci gaba da bayyana irin nasarorin da KRPC ya samu a cikin 2017.

Darakta Abdullahi Idris ne ya wakilci Babban Daraktan a wurin taron.

Share.

game da Author