’Yan fashi da makami sun kutsa cikin gidan Shugaban Kungiyar Kwadago na jihar Ebonyi, suka sace duk wasu kaya masu daraja, sannan kuma suka yi awon gaba da matar sa.
An kai masa wannan harin ne a gidan sa da ke unguwar Mile 50 a Abakaliki, babban birnin jihar.
An ce maharan su biyar ne, su na dauke da bindigogi, kuma sun kai harin ne ranar Lahadi da dare. Rahotanni sun kuma nuna cewa har kudi sun karba su ka yi awon gaba da su.
Shugaban mai suna Mr. Nkah, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an kai harin, amma lokacin da barayin su ka je gidan, shi ba ya nan.
“Mata ta ce ta kira ni ta waya, wajen 9 na dare, ta ce barayi sun je gidan mu, sun nemi inda na ke. Su ka ce sun samu labar akwai kudi a gida na. Don haka a ba su kudin. Su ka tilasta ta kwanta rub-da-ciki, duk da cewa ta na da tsohon ciki.
“Sun yi wa gida na kaca-kaca, su ka yi awon gaba da duk wani abin da za su iya dauka. Amma ba su samu kudin da su ka ce wai an fada musu na shiga da su ba.”
Ya nuna takaicin yadda suka arce tare da matar sa, amma daga baya suka jefar da ita a cikin daji suka gudu.
Discussion about this post