Kwamandan Yaki da Boko Haram mai barin gado, Ibrahim Attahiru, Kwamandan Operaton Lafiya Dole, ya bayyana yadda a karkashin jagorancin sa su ka kashe rikakkun kwamandojin Boko Haram biyar tare da wasu dakarun kungiyar su 70 a cikin wanu dan lokaci.
Ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke mika jagorancin rundunar ga sabon kwamandan da aka nada, Rogers Nicholars, a Barno.
Manjo Janar Attahiru, ya karbi jagorancin rundunar ce tun cikin watan Mayu 2017, amma kuma an cire shi kwanan nan a cikin Disamba.
Sai dai kuma duk da wannan bayanin nasarori da Janar Attahiru ya ke ikirarinn ya samu, yawan hare-hare daga bangaren Boko Haram sun kara kamari tun bayan zaman sa jagoran Operation Lafiya Dole sun kuma rika tayar da bama-bamai, musamman ta hanyar amfani da kananan yara mata, tsakanin Mayu zuwa Disamba.
Ya ci gaba da cewa ya yi nasarorin murkushe hare-haren Boko Haram tare da kai musu hari sosai su na murkushe Boko Haram a mabuyar su. Sai kuma irin hanzarin kai daukin da ya ce an rika yi wajen kwashe al’ummar da ke zaune inda ke da barazanar Boko Haram da kuma ceto da dama daga hannun Boko Haram, bayan an yi bata-kashi da ‘yan ta’addar.
Discussion about this post