Yadda Barcelona ta yagalgala Madrid

0

Kungiyar kwallon kafa ya Barcelona ta yi wa dadaddiyar abokiyar adawarta a kwallo, Real Madrid cin ba sani ba sabo a wasar El-classico da aka buga yau.

Barcelona ta lallasa Madrid ne da kwallaye 3 ba ko daya.

Suarez, ne ya fara jefa kwallo a ragar Madrid bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Ana nan ana ta doka Tamola, sai ko mai tsaron bayan Madrid, Cavajal ya nemi rikidewa goli, inda ya nemi taro kwallo da hannun sa a ragar Madrid. Alkalin Wasa kuwa ya ba Barcelona bugun daga Kai sai gola.

Gogan Barcelona, Leo Messi, ya zura na biya.

Gab da ko za a hura tashi Alex Vidal kuwa ya narka wata Duma inda sai dai kallo, tayi ta zillo har ta shige ragar Madrid.

Daga nan ko alkalin Wasa ya hura tashi.

Share.

game da Author